(ABNA24.com) Kwamitin Shari’a na Majalisar Wakilan Amurka da jam’iyyar Democrat ke da rinjaye, ya fara zaman bahasi na yunkurin tsige shugaban kasar Donald Trump daga karagar mulki.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Jerry Nadler Shugaban kwamitin shari'a na Majalisar wakilan Amurka na cewa idan har shugaba Trump zai iya amfani da karfi iko wajen watsi da dukkanin bukatun 'yan Majalisa, to Majalisar ba za ta iya aiki da nauyin da ya rataya kanta ba wajen sai ido game da bangaren zartarwa ke yi , sannan za ta kalle shi a matsayin shugaban 'yan kama karya.
Ana tuhumar shugaba Trump da abubuwa guda biyu, na farko amfani da karfin iko wajen yiwa gwamnatin kasar Ukrene matsin lamba na gudanar da bincike kan abokin hamyarsa Joe Biden da kuma hana gudanar da bincike kan wannan batu.
Muddin Kwamitin Shari’ar ya kada kuri’ar amincewa da ayoyin biyu na tuhumar Trump a cikin cikin 'yan kwanakin nan , to babu shakka za a gabatar da ayoyin dokar ga zauren Majalisar Wakilan domin kada cikakkiyar kuri’a.
Da zaran Majalisar Wakilan ta amince, to ita ma Majalisar Dattawa wadda jam’iyyar Republican ke da rinjaye a cikiinta, za ta tuhumi shugaba Trump, watakila nan da farkon watan Janairu mai zuwa.
/129
14 Disamba 2019 - 04:44
Lambar labari: 993506
Kwamitin Shari’a na Majalisar Wakilan Amurka da jam’iyyar Democrat ke da rinjaye, ya fara zaman bahasi na yunkurin tsige shugaban kasar Donald Trump daga karagar mulki.